Kamfanin dillancin labaran IQNA, ana shirin gudanar da zaman taro kan musulunci na daliban jami’oi a kasar Ghana a daidai lokacin da za a gudanar da irin wannan taroa biranaen Kano da Lagos da ke Najeriya.
Babbar manufar taron dai ita ce kara wayar da kan daliban jami’oi na kasashen Afrika kan hakikanin koyarwar addinin mulunci, da sahihin tarihin muslunci, da yadda ya kamata musulmi su himmatu wajen samar da ci gaban kasashensu da al’ummominsu.
Daliban jami’oi daga kasashen najeriya, Ghana, saliyo, Ugaganda, Liberi, Gambia da dai sauransu ne za su halarci zaman taron wanda zai gudana a kasahen na Ghana da kuma Najeriya a cikin mako mai zuwa.
A baya an gudanar da irin wannan taro a birnin Accra na kasar Ghana, wanda ya samu halartar daruruwan dalibai daga kasashen Afrika da dama.